[Gist] Wani ƊDan-Daudu dake yaudarar samari ya shiga hannu a garin MInna, kalli yadda aka kwashe

Asirin wani dan daudu daya shahara wajen damfara tare da yaudarar samari a jihar Neja ya tonu, inda aka kama shi yayin dayake kokarin ya sake damfarar wani.

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani na facebook, Fodio Makun ne ya bayyana haka a shafinsa, inda yace wannan dan daudu ya shiga hannu ne a kauyen Shanu dake karamar hukumar Bosso, cikin garin Minna.

Majiyar ya kara da cewa an kama Dan Daudun ne yana sanye da rigunan mama guda shidda, da kuma dan kamfai guda uku, kamar yadda mutanen da suka cika hannu da shi suka gano.

A wani labarin kuma an sake kama wani mutum dake shiga mata, kuma ya kwashe tsawon lokaci yana aiki a wata ma’aikatar gwamnatin jihar Neja, inda yake amfani da sunan mata.

Shi dai wannan dan daudu ya gamu da tasku ne a ranar dayake cikin aiki, sai kayansa suka zube daga cikinsa, a nan aka gano ashe namiji ne ya badda kama.

Latsa nan Domin kallon Hotuna